A cikin wata wasika da ya aike wa mukaddashin shugaban kasar ta Uzbekistan Nigmatilla Yuldashev a jiya Juma'ar shugaba Ruhani ya bayyana alhini da juyayinsa ga iyalan tsohon shugaban, gwamnatin kasar da kuma dukkanin al'ummar kasar Uzbekistan din saboda rasuwar shugaba Islam Karimov.
A jiya Juma'a ce gwamnatin kasar Uzbekistan din ta sanar da cewar shugaban kasar Islam Karimov ya rasu yana dan shekaru 78 sakamakon bugun zuciya da yayi sanadiyar shanyewar jikinsa.
A yau Asabar ne ake sa ran za a yi jana'izarsa a garin Samarkand kamar yadda shari'ar Musulunci ta tanada kana kuma a rufe shi a wajen.
Shugaba Islam Karimov dai ya mulki kasar Uzbekistan din na tsawon shekaru 27.